Tsakure
A yau, kamar yadda Duniya take
tsukewa ta fuskoki da dama, musamman ta fuskar sadarwa, haka ma harsuna suke haɗewa. Nijeriya ita ce ƙasa ta
biyu a duk faɗin
Duniya da take da yawan harsuna, a inda Arewacin ƙasar ake da yawan harsuna fiye da kowane
yanki na ƙasar.
Harshen Hausa da na Fulfulde su ne manyan harsuna na yankin Arewa. Zama tare na
tsawon lokaci na waɗannan
manyan harsuna biyu ya sanya suka haɗe
suka gina al’umma da ake kira da Hausa-Fulani. Wasu daga cikin Hausawa ko
Fulani ko kuma wasu ƙabilun suna haɗa
ƙungiyoyi
domin nuna ƙiyayya
ga wannan al’umma ta
Hausa-Fulani saboda wasu dalilansu, misali: wata ƙungiya da take kiran kanta ‘Hausawa Zalla Development
Association’, wadda
take da rassa masu manufa irin nata da suke da sunaye daban-daban kamar:
Hausawa Mu Farka, Hausawa Mun Farka, Hausawa Gari Ya Waye, Hausa Zalla, da
Fulani Most Go da sauransu. Manufofin waɗannan
ƙugiyoyi
su ne kamar: birkita tarihi, da nuna ƙiyayya ga addinin Musulunci, da kuma nuna
ƙiyayya
ga al’ummar Fulani.
Manufar wannan takarda ita ce fito da yadda al’umma take samuwa ta fuskar
tarihin ilimin harsuna kamar sauyin harshe, da ilimin tarihin zamantakewar ɗan’Adam kamar auratayya, da
kuma ilimin walwalar harshe da ƙulluwar zumunci tsakanin harsuna. Daga ƙarshe,
takardar ta bayar da shawarwari a kan yadda za a magance wannan matsala ta nuna
ƙiyayyar
kamar haka: kafafen sada zumunta su inganta hayoyin tace abubuwan da ake
wallafawa, da al’umma
su yi gangami na yaƙi da tarihihi, da gwamnati ta inganta manhajojin makarantu, da
bin hanyar shari’a, da kuma tattaunawa.
DOI: https://www.doi.10.57233/djfafais.2026.v22i01.009
author/Aminu, A.; Busa, M. A. da Shede, A.
journal/Degel 22(1) | October 2026 |

