Nazarin Hausar Yamma ta Fuskar Ginin Jumla

     Tsakure

    Nazarin karin harshe wani ɓangare ne a cikin nazarin harshe wanda yake ƙoƙarin kwatanta nau’o’in kare-karen harshe masu kusanci da juna ta kammani tare da fitowa da wuraren da suke da bambanci. Masana sun rarraba kare-karen harshen Hausa zuwa manyan yankuna biyu - na Gabas da na Yamma. An yi wannan rabon ne ta la’akari da muhalli da kamannin kare-karen harshen ta fuskar nahawu. Ana iya auna bambancin karin harshen Hausa na yanki a matakin gundarin sauti da tsarin sauti da ƙirar kalma da ginin jumla da kuma ma’ana (ta kalmomi). A kan haka wannan bincike ya yi ƙoƙarin faɗaɗa karin harshen Hausar Yamma ta hanyar zurfafa bincike a kan nau’o’in kare-karensa na Zamfarci da Kabanci da Arauci da Gobirci da kuma Adarci. Bisa ga haka ne wannan maƙalar ta yi ƙoƙarin amsa tambayar “Waɗanne ne siffofin ginin jumla na Hausar Yamma?” An amsa tambayar ta hanyar bincike cikin al’ummomi daban-daban na waɗannan yankuna na kare-karen harshen Hausa na Yamma ta hanyar shirya takardar amsa tambaya da kuma ziyarar waɗannan yankuna domin tattaunawa da wasu daga cikin al’ummomin. An ɗauki waɗannan zantuka a rikoda, aka nazarce su domin cimma manufar binciken. Sakamakon binciken ya gano cewa ana samun bambanci a kare-karen Hausar Yamma ta hanyar ƙarin ɗafin –n tsakanin wasu kalmomin wakilin suna da lamirin lokaci mai nuna kammala aiki; da nason baƙin –z bayan wakilin suna da lamirin lokaci mai-ci; da kuma amfani da dirka a wakilin suna da manuni da kalmomi masu nuna nisan wuri da sauransu..

    DOI: https://www.doi.10.57233/djfafais.2026.v22i01.006

    author/Nazir Ibrahim Abbas & Jamilu Ibrahim Mukoshy

    journal/Degel 22(1) | October 2026 |

    Pages