Abokantaka a Zamantakewar Hausawa

    Tsakure

    Abokantaka a zamantakewar Hausawa lamari ne da ya shafi kusanci da yarda da juna, hakan kuma shi ne yake haifar da riƙon amana a tsakanin waɗanda tasu ta zamo ɗaya. Manufar wannan maƙala shi ne fito da gurbin abokantakar Hausawa a farfajiyar al’ada. An yi wannan yunƙuri ne saboda a fayyace yadda yanayin abokantaka take a ƙasar Hausa. Nazarin ya yi amfani da hanyoyin hira da tattaunawa da kuma karance-karancen ayyuka daban-daban da magabata suka gudanar, domin ganin haƙar sa ta cimma ruwa. Binciken ya yi amfani da karin maganar Hausawa da take cewa: “Kowace ƙwarya tana da abokiyar burminta” a matsayin hanyar ɗora aiki. Sakamakon wannan maƙala ya gano cewa, akwai nau’o’in abokantaka guda uku da suka haɗa da: Abokin arziki da na wucin-gadi da kuma na tsiya. Haka kuma, nazarin ya gano cewa, aboki yana taka muhimmiyar rawa wajen ɗorewar abokantaka.

    DOI: https://www.doi.10.57233/djfafais.2026.v22i01.008

    author/Abdullahi, I. S. S. da Maikwari, H. U.

    journal/Degel 22(1) | October 2026 |

    Pages