Hanyoyin Nazarin Ƙirar Kalma da Siffofinsu

    Tsakure:

    Wannan maƙala  ta yi nazari ne a kan hanyoyin nazarin ƙirar kalma da siffofin nazarin ƙirar kalma a Hausa. Masu hikima suna cewa, sanin hanyar samun kuɗi ya fi kuɗi! Hockett (1954) ya fito da hanyoyi uku na nazarin kalmomin harshe, waɗanda suka ƙunshi: (a) amfani da ƙwayar kalma (b) amfani da dokoki (c) amfani da hanyar jeranta kalmomi cikin sahu. Haka ma, Stump (2001) ya faɗaɗa ta hanyar yi wa hanyoyin Hockett ( 1954) kwaskwarima. Inda ya kawo nasa guda huɗu: (a) amfani da tubalai ko (b) ƙari ko (c) bambantawa ko (d) keɓantacciyar doka. Har wa yau, Haspelmath (2002) ya kawo siffofi huɗu da ya kamata bayani na wata matsala na ilimin ƙirar kalma ya siffantu da su (idan so samu ne). Siffofin su ne: (a) zaɓaɓɓun misalai (b) bayanin kada ya saɓa wa hankali (c) ana buƙatar misalai daga wasu harsuna (d) zayyana hoton yadda matsalar take faruwa. A ganin wannan maƙala, kawo waɗannan batutuwa a nazarin ƙirar kalmomin Hausa, zai cika wani giɓi wanda zai faɗaɗa gonar nazarin ƙirar kalma.

    DOI: https://www.doi.org/10.57233/djfafais.2026.v22i02.005

    author/Isah Abdullahi Muhammmad

    journal/Degel 22(2) | October 2026 |

    Pages