Tsarin Majalisar Sarkin Kano: Jiya da Yau

    Tsakure:

    Manufar wannan bincike ita ce zaƙulo yadda tsarin Majalisar Sarkin Kano take a jiya da kuma yau. An gina binciken a kan manya maƙasudai guda uku da suka hada da; Gano tsarin majalisar Sarkin Kano a jiya da yau. Fito da muƙaman majalisar Sarkin Kano a jiya da yau. Zaƙulo matsayinsu da ayyukansu a majalisar Sarkin Kano a jiya da yau. Sannan an shimfiɗa tambayoyin bincike da ake ganin idan an amsa su daidai, hakan zai nunan cewa an aje ƙwarya a gurbinta. An ɗora wannan aikin kan ra’in tsarin al’adu ko yanayin al’adu (Cultural Scheme Theory). An ɗauki masarautar Kano a matsayin tushen bayani na farko. Tushen bayani na biyu da binciken ya yi aiki da shi, shi ne rubuce-rubucen masana  kan masarautar Kano da suka gabaci wannan bincike. Aikin ya tabbatar da cewa tsarin majalisar Sarkin Kano a jiya ya bambanta da tsarin majalisar na yau. Sannan, takardar ta gano cewa muƙamon ‘yanmajalisar Sarkin Kano a jiya, wasu sun yi canjaras da na yau, yayin da wasu kuma suka yi hannun riga. Daga ƙarshe binciken ya bankaɗo matsayi da ayyukan ‘yanmajalisar Sarki a masarautar Kano.

    DOI: https://www.doi.org/10.57233/djfafais.2026.v22i02.007

    author/Musa Suleiman

    journal/Degel 22(2) | October 2026 |

    Pages