Tsakure
Kafi tsohuwar al’ada ce da ta
shafi tsaro wadda Hausawa suka gada tun iyaye da kakanni, wanda sukan yi tare
da amfani da wasu hanyoyi domin samar wa kawunansu tsaro ta hanyar kafi ko
riga-kafi a muhallansu na gida da gonaki da dabbobi da wuraren sana’o’insu da
iyali da sauransu. Hausawa sun yi imani da kafi, domin kuwa a gargajiyance
kusan kowane Bahaushe kan yi ƙoƙari domin samar da kariya ga muhallinsa
daga cutarwa ko ɓarayi
ko iskoki ko wata annoba da makamantansu. Hausawa kan yi kafi saboda
mabambantan dalilai da suka haÉ—a
da: Neman kariya da neman buwaya da neman waraka da kuma jawo alkairi a
muhallansu. Yin kafi ga dukkan wani lamari yana nuna jarumta da kulawa tare da
nuna ƙwazo
ga mutum. A gargajiyance Hausawa sun É—auki
mutumin da ya kasa kafe muhallinsa kamar gida ko gona ko wurin sana’a ko wani
abu da ya mallaka a matsayin ragon namiji. Babbar manufar wannan bincike ita
ce, fito da nau’o’in kafe-kafen da ake da su da kuma yadda ake aiwatar da su,
sannan an yi amfani da hanyoyin neman bayanai, wajen tattaunawa da masana
daban-daban domin samun ingantattun bayanai..
DOI: https://www.doi.10.57233/djfafais.2026.v22i01.010
author/Aliyu Mu’azu & Ahmad Muhammad Mika’il
journal/Degel 22(1) | October 2026 |

